A ranar juma’a ne kamfanin Nvidia yayi kiranyen duk na’urorin ‘Shield table’ da ya sayar tsakanin watan Yuli na shekara ta 2014 da Yulin shekara ta 2015, tsawon shekara guda kenan.
Kamfanin dai yace batirin da ke jikin na’urar table din ya zamanto yana da matsala domin yana ‘daukan zafi sosai, wanda hakan ka iya kaiwa ga kamawa da wuta. Kamfanin dai yace babu wasu kayayyakin su dake da matsala kamar akwatin talabishin da sauran kayayyakin wasannin game, kuma sunyi kiranyen wannan na’ura ne bisa ra’ayin kansu.
Nvidia ya fitar da bayanin cewa duk na’urar da ke da batiri mai lamba B01 to wannan kiranye bai shafe su ba, amma duk wanda yake da mai lamba Y01 to yayi maza-maza ya dawo da ita inda ya saya.
Hukumar kula da kayayyakin da ake sayarwa da jama’a ta tabbatar da cewa an sayar da Shield tablet dubu tamanin da uku a Amurka, san nan an sayar da dubu biyar a kasar Canada.
Fitatcen kamfanin Nvidia wanda yayi fice wajen yin na’urori masu kwakwalwa, a baya ne ya kirkiri karamar na’urar ‘Shield tablet’ domin masu wasan game.
Cibiyar kamfanin dai na jihar California a Amurka, har yanzu dai bai fitar da rahotan ko na’urar nawa ya sayar a kasuwa, masana harkokin fasaha na ganin dai kamfanin bai sayar da na’urar da ya waba, domin a halin yanzu mutane basu fiye sayen ire iren wadanna na’urorin ba, koda kuwa irin na manya manyan kamfanoni ne kamar su Apple ipad.