Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Kasuwanci Boko Sai Manajan Banki


Matasa
Matasa

Dogaro da kai wata kalma ce da akan yi amfani da ita a wasu lokutta, wanda take nufin abubuwa da dama. Sau da yawa wasu kan dauki cewar, sai kana sana’ar kanka shine kake kokarin dogaro da kanka. Wanda bahaka wanna maganar ta ke ba, kamar yadda Musbahu Umar, mai kimanin shekaru ashirin da biyu, yake nuni da cewar ya kasan ce yana tsaron shagon wani dan’uwan shi, a lokacin da ya dawo daga makaranta, kana kuma yana karatu, domin kuwa a nashi fahimtar karatu, sai mutun nada goyon baya kamin yasamu ya iya kammala karatu, musamman ma na gaba da sakandire.

Domin kuwa karatun a kowane mataki na bukatar kudi da sauran abubuwan more rayuwa. A bisa wanna dalilin ne yasa yake wanna aikin na tsaron shago, kana kuma yaje makaranta. Duk don burinsa na ya samu ya zama mai nashi jari a gaba. Don ya fahimci cewar, babu yadda za’ayi mutun ya iya zama wani abu a rayuwa, batare da jingina da wani ba. Musbahu dai na karatu a fannoni uku, fannin tsarin Ajiya, kasuwanci, da tsimi da tanadi, wanda idan Allah yasa ya kammala, yana sha’awar aikin Banki, domin kuwa wanna aikin yana bashi sha’awa matuka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG