Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Ware $ Trillion 7 Dan Wani Sabon Shiri


A taron da ofishin muradun karni ya shirya a Abuja, kan wannan shirin da Majalisar Dinkin Duniya ke kula dashi, karewar wannan shirin yasa za’a kafa wani sabon shirin a watan gobe, mai suna “Sustainable Development Goals” da zai yi aiki zuwa shekara ta 2030.

Tuni aka tsara cewa dalar Amurka Billion dubu bakwai ake bukata da samar da ababen more rayuwa da kuma wasu miliyan dubu bakwai duk shekara domin yaki da talauci.

Mansur Manu Shoro, mai baiwa Gwamna Bauchi shawara akan wannan shirin yace “ masana sun yi kiyasin cewa akwai muradu da za’a sake kawowa guda goma sha bakwai, kuma an riga anyi mahawaran yadda za’a samu kudaden gudanar da su tambayar dake bakin mutane yanzu shine bayan anyi shekaru goma sha shida ana gudanar da shirin muradun karni, shin mata da suke mutuwa wajen haihuwa a bayan sun daina mutuwa shin an samu Karin yara a makarantu masamman makarantar friramari.”

Ci gaba dai za’a iya cewa an samu amma har yanzu akwai damuwa da yawa wanda ake fuskanta wanda ita kuma Majalisar Dinkin Duniya tana kokarin kawo Gwamnatocin duniya domin ayi wana taron a ga kuma cewa ita wannan sabon shirin ya fara aiki a shekara ta 2016.

Idan har za’a cimma nasara akan wandannan muradu inji daraktan tara gudumawar kamfe na shugaba Buhari, wato Ibrahim Abdulkareem sai an farfado da aikin hukumar wayar da kan jama’a NOA.

XS
SM
MD
LG