Iyalan wani mutumin dake da zama a Jihar Alabama a nan Amurka, sun yi tattaki har zuwa Jihar Colorado a cikin mota, domin karbo wani karensu mai suna Boozer, wanda ya bata shekaru 9 da suka shige.
Boozer, wanda ayanzu shekarunsa na haihuwa 10 ne, ya bace a lokacin da iyalan suka yi kaura daga Jihar Tennessee zuwa Alabama.
Gidan telebijin na KUSA-TV ya ba da rahoton cewa mutumin da wannan kare Boozer yake hannunsa ya kaura zuwa birnin Denver a Jihar Colorado kwanakin baya, kuma sai ya mika wannan karen ga wani gidan kula da dabbobi mai suna Foothills Animal Shelter dake garin Golden a ranar 2 ga watan nan na Agusta. Mutumin yace ba ya da karfin da zai iya kula da karen a yanzu.
Wannan gidan kula da dabbobi ya duba wata na'urar dake makale a wuar Boozer, sai ya gano cewa asalin wanda yayi rajistar karen a zaman nasa sunansa Lloyd Goldston dake da zama a Jihar Alabama.
Goldston yace har yanzu yana da littafin hotunan Boozer tun yana dan karami, kuma har zuwa gobe ba su taba mantawa da shi ba. Goldston da 'ya'yansa biyu, sun yi tukin mota na tsawon awa 18, inda har hawaye ya rika zuba masa a lokacin da yayi ido hudu da wannan kare nasa da ya bace shekaru 9 da suka shige.