Kudirin gudanar da garanbawul ga kundin dokar gudanar da wa’azi ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokoki ta jihar Kano kuma har ma majalisar ta umarci kwamitin ta kan harkokin addini ya ji ra’ayin jama’a, musamman Malamai game da yadda ya kamata kundin dokar ya kasance.
Wannan dai shine karo na biyu da majalisar zata gudanar da sauye sauye a tsarin kundin dokar cikin shekara daya da ‘yan watanni.
A shekara 1985, ne Gwamnatin Gwamnatin mulkin soja ta wallafa kundin dokar da nufin sanya linzami ga masu gudanar da wa’azi , a fadin jihar Kano.
Bangaren zartarwa na Gwamnati ne ya mika daftarin dokar ga zauren majalisar dokokin ta Kano, domin majalisar ta gudanar da gyare gyare a sashin na goma sha takwas karamin kasha na daya da na biyu, wandanda suka tanadi amincewar hukumomin Gwamnati kafin Malami ya gudanar da wa’azi.
Baya ga wajabta kaucewa lafazi na tunzura jama’a, da batanci ga wani ko wasu a matsayin sharuddan gudanar da wa’azi, sansan guda biyu na dokar sunyi tanadin tara ko dauri a gida kurkuku ga duk Malami da aka kama yak eta kaidojin da dokar ta shinfida.
Bayan mahawara akan wannan kudiri majalisar dokokin ta Kano, ta umarci kwamitin dake kula da lamuran addini da ya tuntubi masu ruwa da tsaki masamman ma majalisar Malamai da masauratar Kano da sauran su.