Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canji Ba Zai Yuba Sai an Kawo Matasa


Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kowace ranar 12, ga watan Agusta, a matsayin ranar matasa ta duniya .

Sakataren janar na Majalisar Banki Moon, yace gudumawar matasa a wazuwar zaman lafiya da kuma ci gaban al’uma shine mafi a’ala.

Shi kuwa shugaban kungiyar matasan Najeriya, Abubakar Dangulguli, yace ” wanna rana ce da matasa zasu tabbatarwa da duniya, cewa an bar matasa a baya a harkokin siyasa da na tattalin arziki wanda yakamata ace matasa ne ke jagora wajen hadin kai a duniya da kuma kasashen su dan ci gaba da kumazaman lafiyar kasashen su.”

Ya kara da cewa yanzu ne yakamata Gwamnatocin kasashen duniya suyi amfani da matasa ta hanyar basu abun yi da ilimi da kuma tabbatar da cewa sun taimaka masu saboda kada a sa kasahen duniya a cikin tashin hankali.

Ya kuma yi kira ga hukumomin Najeriya, da kasashen duniya cewa yakamata kada a bar Matasan Najeriya kara zube basu da amfani sai lokacin siyasa zo a basu kwayoyi su sha suyi rashin mutunci, kuma an jefar dasu kennen sai bayan shekara hudu.

Saboda yace yakamata a baiwa matasa sanao’I na hannu wanda zasu taimaki kansu su taimaki kaasar su saboda su kawo hadin kan kasa.

Yakamata wannan Gwamnati wace take ikirarin canji, canjin nan bazai yuba sai an kawo matasa an dama dasu saboda su zasu rike kasar gobe.

XS
SM
MD
LG