Sheinbaum ta kasar Mexico ta samu gagarumin rinjaye inda ta zama mace ta farko da ta zama shugabar kasar inda ta gaji aikin jagoranta kuma shugaba mai barin gado Andres Manuel Lopez Obrador wanda shahararsa a tsakanin talakawa ya taimaka mata wajen samun nasarar.
Sheinbaum, masanin kimiyyar yanayi kuma tsohuwar shugaban birnin Mexico, ta lashe zaben shugaban kasa da kashi 58.3% zuwa 60.7% na kuri'un da aka kada, bisa ga wani saurin kididdigar da hukumar zabe ta Mexico ta yi.
Wadda ke biye mata a matsayi na biyu da kashi 29 cikin 100 na kuri'un ita ma mace ce, mai suna Xochitl Galves, fitacciyar 'yar kasuwa kuma 'yar majalisar dattijai yanzu haka.
Wanda ke a mataki na uku ne dai namiji mai suna Jorge Alvarez Maynez, mai kashi 11 cikin 100 na kuri'n zaben.
"A karon farko a cikin shekaru 200 na jamhuriyar, zan zama mace ta farko da ta zama shugabar kasar Mexico," Sheinbaum ta fadawa magoya bayanta