WASHINGTON, D. C. - A wannan zabe mai ban mamaki ana dai sa ran daya daga cikin mata 'yan takara biyu ta zama mace ta farko da za ta shugabanci kasar.
A wani zaben sharar fage da aka gudanar a ranar jajibirin kada kuri’ar, 'yar takarar jam’iyya mai mulki Claudia Sheinbaum, tsohuwar magajiyar birnin Mexico kuma masaniyar ilimin kimiyya, ta samu nasara da kashi 17 daga cikin 100 kan babbar abokiyar hamayyar ta Xochitl Galvez.
Sheinbaum mai shekaru 61 a duniya, ta shaidawa manema labarai, kafin ta zarce zuwa wata mazaba da ke babbn birnin kasar, Mexico city, cewa, wannan rana ce mai cike da tarihi, kuma tana cike da farin ciki, inda tayi fatan Allah ya daukaka demokaradiyya, bayan ta kammala kada kuri’ar ta.
Namiji daya tilo da ke cikin jerin 'yan takarar Jorge Alvarez Maynez ne ya kasance a baya kwarai, a kuri’ar da aka kada.
Dandalin Mu Tattauna