Nadin nata ya kawo karshen tsawon makonni na rashin tabbas. Bikin rantsar da Tshisekedi a wa'adi na biyu a watan Janairu, ya fara ne bayan an ja dogon lokaci wajen neman kafa kawancen da ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar, wani muhimmin mataki kafin a nada firaminista da kuma kafa gwamnati.
"Ina sane da babban nauyin da ke rataya a wuya na ... Za mu yi aiki don samar da zaman lafiya da ci gaban kasa," in ji Suminwa a gidan talabijin na kasa.
Hukumomin kasar na fuskantar kalubale da dama da suka hada da tashe- tashen hankula da rikicin jin-kai a yankunan gabashin kasar da kuma kula da dumbin arzikin ma'adinai na Congo.
A wa'adinsa na farko, Tshisekedi ya yi alkawarin kawar da matsalar cin hanci da rashawa, da sake gina tattalin arziki, da magance rashin daidaito da kuma dakile matsalar tsaro a gabashin kasar, amma masu sukar lamirin sun ce ya gaza ta kowane fanni.
Dandalin Mu Tattauna