Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Da Trump Za Su Ziyarci Iyakar Amurka Da Mexico Rana Guda


Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump

Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump za su nufi kan iyakar Amurka da Mexico a cikin wannan mako, inda za su maida hankali  kan daukar matakan gaggawa dangane da  cigaba da  kwararar dubun dubatan bakin haure da ke ke shigowa Amurka.

Kwararar bakin haure dai lamari ne mai cike da cece-kuce da tabbas zai zama babban batun da za a yi muhawara a kai a zaben kasa na watan Nuwamba.

Biden da Trump dai sun sha yin sukar juna kan dokar shige-da-fice tun ba yanzu ba a tarukan yakin neman zabe a jihohi daban-daban, inda su ke zargin juna da kwararar bakin haure.

(FILES) US President Joe Biden speaks with US Customs and Border Protection officers as he visits the US-Mexico border in El Paso, Texas, on January 8, 2023.
(FILES) US President Joe Biden speaks with US Customs and Border Protection officers as he visits the US-Mexico border in El Paso, Texas, on January 8, 2023.

Amma a ranar Alhamis, za su kasance kusan kilomita 500 (kimanin mil 311) da juna, in da Biden zai nufi Brownsville da ke Texas, don ganawa da jami'an sintiri na kan iyakoki na Amurka, da jami'an tsaro da shugabannin yankin kuma Trump zai nufi Eagle Pass da ke Texas, daya daga cikin wuraren shigar bakin haure mafi girma.

Trump-Border Visit
Trump-Border Visit

Dukansu Trump da Biden suna kokarin nuna cewa, kowannensu shine, ko kuma zai kasance, shugaban da zafi daukar matakin shawo kan kwararar bakin haure a sabon wa'adin shugabancin da zai fara a watan Janairu mai zuwa.

Trump a lokacin da yake yakin neman zaben da ya yi nasara, a shekarar 2016 ya yi ikirarin cewa zai gina katangar kan iyaka kuma zai sa Mexico ta biya ta. An kuma gina wani bangare a lokacin shugabancinsa, sai dai ba Mexico ba ta biya ba.

A yakin neman zabensa na 2020 da ya yi nasara kan Trump, Biden ya ce zai dauki matakan shawo kan kwararar bakin haure na mutunci, amma yanzu, tare da dubban bakin haure da ke zuwa kowane mako a kan iyaka, an tilasta masa daukar tsauraran matakai.

Biden ya ce zai goyi bayan shawarar shawarar da za a bayar a Majalisar dattijai ta bai daya ba tare da banbancin siyasa ba, don shata sabbin ka’idojin shige da fice, amma ba a kai ga kafa dokar ba musamman lokacin da Trump ya ce ba ta da tsauri kuma duk ‘yan jam’iyar Republican da a farko suka yi niyyar goyon bayan tsarin ya bi umarnin Trump, ya ja da baya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG