Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mace Ta Farko Da Ta Tsayawa Takarar Shugabancin Senegal Ta Zama Abin Koyi


Anta Babacar Ngom
Anta Babacar Ngom

'Yar takarar shugaban kasa mace daya tilo a Senegal wadda da alamun ba za ta yi nasara ba a zaben ranar Lahadi, amma masu fafutuka sun ce fitowarta takara zai taimakawa wajen ci gaban yakin neman zabe don cimma daidaiton jinsi a kasar da ke yammacin Afirka.

Anta Babacar Ngom, 'yar shekara 40 mai kula da harkokin kasuwanci, murya ce ga mata da matasa, kungiyoyin da ke fama da matsalolin tattalin arzikin kasar, da rashin aikin yi da tashin farashin kayayyaki. Ta yi alkawarin samar da miliyoyin ayyukan yi da kuma bankin mata don tallafawa 'yancinsu na tattalin arziki.

“Kasarmu tana da fa’ida sosai. Albarkatun kasa suna nan, kuma za a iya bunkasa su,” kamar yadda ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press. “’Yan matan da na hadu da su suna neman tallafi na. Suna yin haka ne domin sun san idan mace ta hau mulki za ta kawo karshen wahalar da suke sha. Ba zan manta da su ba."

Anta Babacar Ngom
Anta Babacar Ngom

Kadan ne ke sa ran Ngom za ta kasance cikin manyan ‘yan takarar shugabancin kasar, sai dai masu fafutuka na ganin cewa tun da har mace ta samu tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar a karon farko cikin shekaru da dama, ya na nuni da yadda mata ke ci gaba a fafutukar tabbatar da daidaito.

"Dole ne a dama da mu, ko da ma mun san ba za mu yi nasara ba," in ji Selly Ba, wata mai fafutuka kuma masaniyar zamantakewa. “Ba mu da wata dama yin nasara a wadannan zabukan. Amma yana da muhimmanci mu sami mata ‘yan takara, mata da ke cikin takara.”

Ngom ita ce mace ta farko da ta tsaya takarar shugaban kasa cikin shekaru goma, lamarin da ke nuni da yadda ci gaba ke tafiyar hawainiya ga masu fafutuka, wadanda suka ce an samu sauyi a tsakanin matasa zuwa ga karin ra'ayoyin gargajiya na mata a cikin al'umma.

Senegal Election Women
Senegal Election Women

A shekarar 2012, mata biyu ne suka tsaya takarar shugaban kasa, kuma yayin da suka samu kasa da kashi 1% na kuri’un da aka kada kowacce, manazarta sun ce shigarsu na da muhimmanci. Mata a Senegal yanzu suna da sama da kashi 40 cikin 100 na kujerun Majalisar dokoki, daya daga cikin mafi girman wakilcin mata a Afirka.

Ngom ta shaida wa kamfanin dillacin labari AP cewa, "Yana da mahimmanci don daidaita tsakanin juyin zamani da mutunta al'adunmu. Dole ne mata su iya bayyana ra'ayoyinsu ba tare da tsangwama ba, tare da kiyaye al'adunmu."

Magoya bayan Ngom sun ce suna alfahari da goyon bayan mace ‘yar takara da kuma fatan samun sauyi a gwamnati mai zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG