Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nikki Haley Ta Janye Daga Neman Tikitin Takarar Shugabancin Amurka Karkashin Jam’iyyar Republican.


'Yar takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican kuma tsohuwar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, yayin da take jawabi da manema labarai a yau Talata, 6 ga watan Maris a jihar South Carolina.
'Yar takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican kuma tsohuwar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, yayin da take jawabi da manema labarai a yau Talata, 6 ga watan Maris a jihar South Carolina.

Nikki Haley Ta kawo karshen yunkurin da take yi na samun tikitin yiwa jam’iyyarta ta Republican takarar shugabancin Amurka.

WASHINGTON DC - Hakan ya biyo bayan rashin nasara da ta yi a jihohi 14 a zabubbukan fidda gwanin da suka gudana a ranar Gagarumar Talata a hannun abokin hamayyarta Donald Trump.

Tsohuwar Gwamnan Jihar South Carolina, wacce ta taba zama Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya a karkashin gwamnatin Trump kuma mace ta farko wacce ba farar fata ba data nemi tikitin takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Republican, ta gabatar hakan ne a yayin wani jawabi a kusa da gidanta na South Carolina da misalin karfe 10 na safiya agogon Amurka a yau Laraba.

Haley ta sha fama da jerin rashin nasara, daya samo asali daga jihohin Iowa da New Hampshire da Nevada harma da jiharta ta asali South Carolina.

A jiya talata, bayan kammala kada kuri’u a jihohi 15 a zabubbukan fidda gwanin da aka yiwa lakani da Gagarumar Talata ko Super Tuesday a turance, Haley tayi rashin nasara a dukkanin jihohin in banda Vermont.

A baya can ta lashe zaben a jiha daya tilo, Washington DC.

A cikin manyan abokan hamayyar Trump, Haley ce kadai ta rage a takarar, don haka janyewarta na bada tabbacin cewar Trump zai samu tikitin takarar jam’iyyarsa ta Republican.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG