Sun kai hare haren ne adaidai lokacin da jama'a ke shirin sallar idi yau da safe a wurare daban daban guda uku.
Ko jiya an kai hari a garin Gombe wanda ya yi sanadiyar mutane kimanin hamsin tare da jika wasu da dama. Harin na yau ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara tare da raunata wasu guda goma sha takwas.
Ana kyautata zaton wasu mata ne suka kai hare haren. Hare haren sun zo ne yayin da sabon hafsa sojoji Manjo Janar Tukur Yusuf Buratei yayi alkawarin yin sallah a garin Damaturu a jihar Yobe da kuma garin Maiduguri, garuruwan da suka y kamarin suna wajen hare haren kungiyar Boko Haram.
To saidai duk da hare haren basu hana mutanen Damaturu halartar msallatan idi ba. Malam Umar Izge wani mazauni garin Damaturu kuma ganao kan irin abubuwan da suka wakana yace wurare biyu ne bamamai suka fashe. Daya a masallacin idi dayan kuma kusa da wani masallaci. Duk 'yan kunar bakin waken mata ne.
Kanal Salihu Usman Kuka jami'in hulda da jama'a na rundunar sojojin Najeriya yayi karin haske akan abun da ya faru yau. Kawo yanzu dai ba'a kama kowa ba amma wai suna bincike.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5