Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IS Ta Kai Hari a Masar


Wani waje da aka yi yamutsutsi a lokacin juyin juya hali a kasar Masar
Wani waje da aka yi yamutsutsi a lokacin juyin juya hali a kasar Masar

Mayakan IS masu da'awar kafa daular musulunci sun kai hari kan wani jirgin ruwan sojin kasar Masar da ke yankin Sinai.

Reshen mayakan IS da ke Masar, ya bayyana kai harin linzami akan wani jirgin ruwan dakarun kasar a arewacin yankin Sinai, wanda hukumar tattara bayanai ta tabbatar.

Hotunan da aka saka akan shafukan intanet sun nuna lokacin da makamin linzamin ya kai ga jirgin ruwan, sai dai babu tabbacin asalin wadannan hotuna.

Sai dai hukumomin kasar ta Masar sun ce jirgin ya kama da wuta ne bayan wata arangama da aka yi da mayaka kuma babu wanda ya jikkata.

A ‘yan kwanakin nan, kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai hare-hare akan shingayen binciken dakarun kasar a yankin Sinai, inda akalla sojoji 64 suka mutu.

Wani babban jami’in kasar ya ce mayakan suna amfani da muggan makamai da basu misaltuwa ciki har da na cilla makamin roka.

XS
SM
MD
LG