Tsohon babban hafsan mayakan Najeriya, Laftanar Janar Kenneth Minimah, ya ce saura kadan kungiyar Boko Haram ta durkusar da rundunar sojin Najeriya.
Minimah ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, ya yin da ya ke mika ragamar tafiyar da rundunar ga Janar Tukur Yusuf Buratai wanda ya gaje shi.
“Lallai kungiyar Boko ta yi daf da durkusar da rundunar sojin Najeriya ta hanyar kai hare-hare akan sansanonin soji ba kakkautawa inda suka kwashe makamai tare da kashe fararen hula da bas u jib a basu sha ba.” In ji Minimah.
A cewar Minimah irin halin da ya samu rundunar sojin kasar ke nan watanni 18 da aka na shi a baya inda ya kara da cewa hakan ya sa gwiwar sojojin Najeriya ta sanyi inda har suke tserewa daga filin daga yayin da sun ji duriyar ‘yan kungiyar.
Ya kuma nuna bakin cikinsa kan yadda ‘yan Najeriya suka kusa yanke kauna ga dakarun kasar saboda irin barnar da kungiyar Boko Haram ta yi a arewa maso gabashin kasar.
Sai dai ya ce a ‘yan watannin akwai alamun ana samun nasara akan ‘yan kungiyar yana mai cewa ana dab da murkushesu.
“Amma ina mai farin cikin sanar da ku cewa yayin da nake shirin barin wannan mukami, kungiyar Boko Haram na dab da durkushewa.”
Ga karin bayani a wannan rahoto da Hassan Maina Kaina ya hada mana: