Wani hari da aka kai da jirgi mara matuki ya halaka wasu mayakan Al Shabab da ake alakantawa da kungiyar Al Qaeda su 30, cikin har da manyan shugabannin kungiyar.
Dakarun Amurka ba su ce komai ba yayin da rahotannin ke cewa su suka kai harin da yammacin jiya Laraba a kusa da garin Bardere da ke yankin Gedo.
Daga cikin shugabannin kungiyar Al Shabab da aka kashe a harin akwai Jama Dere da Ismael Jabhad, in ji kakakin ma’aikatar cikin gida kasar Kenya, Mwanda Njoka.
Wani dan jarida ya gayawa Muryar Amurka cewa mataimakin kwamandan kungiyar Al Shabab a yankin Jubba da Jabhad, tsohon babban soja ne.
Garin na Bardere, mai tazarar kilomita 400 daga kudu maso yammacin Mogadishu, ya kasance wata tunga ta ‘yan kungiyar Al Shabab, inda dakarun hadin gwiwa na Habasha da Somali ke shirin kai wani farmaki domin kwato garin.