Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram: Malamai Sun Yi Kiran Yin Addu’oi


Wasu 'yan Najeriya suna addu'oi
Wasu 'yan Najeriya suna addu'oi

Yayin da ake samun karin hare-hare a wasu sassan Najeriya, shugabannin addinai sun yi kiran a dukufa wajen yin addu'oi domin kawo karshen matsalar Boko Haram.

Shugabanin addanin Islama a Najeriya sun yi kira da a dukufa wajen yin addu’oi domin ganin an kawo karshen tashin hankalin hare-haren kungiyar Boko Haram.

Malaman sun yi kiran ne yayin da ake addu’oi na musamman a babban masallacin tarayya na Abuja, a lokacin rufe tafsiran watan Ramadana.

“Ina kiran ‘yan uwa musamman ‘yan Najeriya a ko ina a masallatai daban daban su yi addu’a na zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa ta mu, su yi addu’a Allah ya kawo mana mafita kan yadda za a warware wadannan matsaloli da su ka dame mu na tsaro a wannan kasa.” In ji Na’ibin limamin babban masallacin, Dr. Kabir Adam.

A wani bangaren, shugabannin al’uma sun kuma yi kira da a gujewa yiwa shugabanni mummunar addu’a domin karshen ta za ta iya dawowa kan masu yin irin wannan addu’a.

“Duk lokacin da mutum ya roki Allah ya halakar da shugabansa to ya yi ganganci.” In ji Dr. Suraj Sabo Keffi.

Ya kuma yi misali da cewa, yin irin wannan addu’a tamkar mutum yana cikin mota ne ya roki Allah ya sa direban ya makance.

“To kaga haka ai ya janyo wa kansa matsala, shi ya sa mu ke cewa mu rika yiwa shugabannin addu’a kuma mu kara juriyar hakuri, domin ba zai yiwu gyaran da muke so a same shi a wata daya ko biyu ko uku kai koma a shekara ba.” Dr. Keffi ya kara da cewa.

Ga karin bayani a rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG