‘Yan Ta'adda Sun Kashe Mutane 32, Ciki Har Da Makiyaya 25 A Jihar Borno 

Wani mutum dauke da gawar danshi da ya mutu sakamakon rikicin 'ya ta'adda

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne da ke da alaka da kungiyar IS, sun kashe mutane 32 da suka hada da makiyaya 25 a wasu hare-hare guda biyu da aka kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.  

An kai hare-haren ne a ranar Talata a yankin tafkin Chadi, inda kungiyar IS da ke yammacin Afirka ke iko da yankuna da yawa.

Mayakan sa kai da ke yaki da ‘yan ta’addan sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, mayakan ISWAP a kan babura sama da goma sun kashe makiyaya 25 a harin farko. Shugaban mayakan na sa kai, Babakura Kolo, ya ce maharan ba su dauki wani abu daga makiyayan da ke kiwo a dajin Gudumbali mai tazarar kilomita 95 daga birnin Maiduguri ba.

Yan bindiga

Yawancin makiyayan an harbe su ne yayin da wasu kuma aka sassare su har lahira, in ji shi.

Mayakan masu tsattsauran ra’ayin addini sun umurci makiyayan da su fice daga yankin, bayan da suka zarge su da ba sojoji bayanai kan ayyukan da suke yi.

A baya-bayan nan kungiyoyin sun zafafa kai hare-hare kan manoman da ke aiki a gonakinsu a lokacin damina. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce akalla mutane 40,000 ne aka kashe yayin da wasu kusan miliyan biyu suka rasa matsugunnansu a rikicin da aka kwashe shekaru 14 ana yi, wanda ya bazu zuwa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru.

~AFP