Tun a watan Mayun da ya gabata ne jihar Filato ta fuskanci yawaitar hare-hare a tsakanin Musulmai makiyaya da kuma al’ummar Kiristoci manoma, a rikicin da karamar hukumar ta ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 300.
Babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, ya ziyarci Mangu da ke jihar Filato a ranar Asabar domin fara gudanar da ayyuka na musamman don kawo karshen rikicin.
Gundumar Mangu na daya daga cikin wuraren da rikicin baya-bayan nan ya barke inda aka yi ta sace-sace a kauyuka tare da lalata filayen noma.
"Akwai kiyasin 'yan gudun hijira 80,000 a cikin sansanoni daban-daban har 11 a karamar hukumar," in ji Markus Artu, wani babban jami'i a gundumar Mangu.
Kimanin mutane 18,000 daga cikin wadanda suka rasa matsugunansu suna samun mafaka a daya daga cikin sansanonin da ke makarantar firamare a garin Mangu.
Daya daga cikin masu kula da sansanin, Yamput Daniel, ya bai wa AFP irin wannan kiyasin.
Kwamandan rundunar tsaro ta ‘Operation Safe Haven’ na yankin Filato ya mayar da hedikwatarsa na wani dan lokaci zuwa Mangu tare da tura karin sojoji 300 da motocin sulke zuwa gundumar.
Ba a kai ga tantance ko me ya jawo barkewar hare-hare na baya-bayan nan a Filato ba.
“Mun gaji da zama a nan, mun yaba da tsaro da ake samu, amma zai fi kyau idan gwamnati za ta tura mafi yawan jami’an tsaro a kauyuka, domin mu dawo,” in ji Mary Ishaya, wata mata da ke zaune a gundumar Mangu. "Amma an bar mu a nan, da 'ya'yanmu, ba abinci, ba magani, kuma yaran ba sa zuwa makaranta."
Dandalin Mu Tattauna