Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 11 A Sabon Rikici A Kudancin Chadi


Yan bindiga
Yan bindiga

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a kudancin Chadi a yankin da ke fama da tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma, in ji sojoji a ranar Alhamis.

Harin dai ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata, a daidai lokacin da kasar Chadi ta sanar da cewa ta shiga cikin makwabciyarta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) a wani farmakin da ba a taba ganin irinsa ba.

‘Yan fashi da makami sun kai hari kauyen Mankade da ke gundumar Laramanaye, inda suka kashe mutanen kauyen 11 tare da sace shanunsu,” Ministan Tsaro Daoud Yaya Ibrahim ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Wasu da aka kashe
Wasu da aka kashe

“Jami’an tsaro sun bi su, inda suka kashe ‘yan bindiga 7 tare da kama wasu guda takwas,” in ji shi. Ya kuma kara da cewa an kwato shanun da aka sace.

Lamarin ya faru ne a kudu mai nisa na babban yankin Sahel, mai tazarar kilomita 60 daga kan iyaka da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Mataimakin shugaban gundumar Laramanaye, Djimet Blama Souck, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kashe mutanen kauyen 12 da suka hada da mata da kananan yara.

A ranar 8 ga watan Mayu, mutane 17 a kauyukan yankin ne suka mutu a wani hari makamancin haka, wanda sojojin Chadi suka dora alhakinsu kan "'yan bindiga" 'yan kasar Chadi da suka tsallako daga CAR.

A ranar Larabar da ta gabata, ministan tsaron kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, a makon da ya gabata dakarunsa sun bi maharan a kan iyakar kasar, da kuma hadin gwiwar sojojin kasar CAR sun kashe kusan goma sha biyu daga cikinsu.

Yanzu haka dai an kawo karshen wannan farmakin, in ji shi a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa, an kashe barayi da dama, kuma sojojin Chadi sun koma gida dauke da fursunoni 30 da shanu 130 da aka sace.

Ba za a iya tabbatar da wannan ikirari da kansa ba a wannan yanki mai nisa, kuma gwamnatin CAR ba ta tabbatar da hakan ba, da cewa sojojin kasashen biyu sun gana "domin kwantar da hankali."

Ana zaman doya da manja tsakanin CAR da Chadi, biyu daga cikin kasashe mafi talauci da tashin hankali a duniya.

Dangantaka dai na da nasaba da zargin junansu cewa kowanensu na da 'yan tawaye masu dauke da makamai.

Tashin hankali dai ya samo asali ne daga kishiyantar filaye.

Sau da yawa manoman na zargin makiyayan da shanunsu da tattake amfanin gonakinsu suna cinye su, yayin da makiyayan suka ce suna da hakkin yin kiwo a can.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG