‘Yan sanda a tsakiyar jihar Nasarawa sun ce ga dukkan alamu kashe-kashen na ramuwar gayya ne kan mutuwar wani bafulatani makiyayi da aka kaiwa hari da adduna. Yawancin rikice-rikice da ke tsakanin manoma da makiyaya kan gonaki, sukan karkare ne da tashin hankali..
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya ce hukumomi sun aike da jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sanda, rundunar yaki da ta’addanci da sojoji zuwa yankin da lamarin ya shafa.
Ya ce rikicin kabilanci tsakanin manoma da makiyaya a yankin abu ne da ba saban ba, kuma hukumomi na tattaunawa da makiyaya da manoma domin yin sulhu, yayin da ake ci gaba da bincike.
Maharan sun mamaye kauyukan Tarkalafia da Kwaja da ke gundumar Karu da yammacin ranar Alhamis inda suka yi ta’addanci kan mutanen kauyen na tsawon sa’o’i kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
‘Yan sanda sun ce harin ramuwar gayya ne bayan da aka kashe wani makiyayi mai shekaru 18 ta hanyar sara masa adda a kai a wannan yanki kwanaki biyu da suka gabata.
Yayin da yake zantawa da Muryar Amurka ta wayar tarho, Nansel ya ce:
“A wannan yankin, wannan karon farko da muka sami irin haka don haka abin mamaki ne. Mun yi kira ga masu ruwa da tsaki da a hada hannu, mun bukaci a yi taro tsakanin manoma da makiyaya a fadin jihar da kuma wasu zababbun kananan hukumomi [yankuna. ] inda muka saba fuskantar waɗannan ƙalubalen."
Mazauna yankin sun shaidawa kafafen yada labaran Najeriya cewa an kashe akalla mutane 38. Sun ce wadanda aka kashen da suka hada da mata da kananan yara an yi jana’izarsu ne a ranar Asabar.
Nansel ya ce a yanzu haka 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 15 kawai.
Rikicin manoma da makiyaya kan albarkatu kamar ruwa, gonaki da ciyawar dabbobi, na daya daga cikin kalubalen tsaro da ke addabar kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka.
A cikin shekarar 2018 Amnesty International ta ce kusan mutane 4,000 ne aka kashe a mummunan fadan da aka shafe tsawon shekaru uku ana yi. Kungiyar ta ce rashin binciken matsalar da gwamnati ke yi ne ta kara ruruta rikicin.
Hukumomin kasar sun aike da ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, inda suka yi alkawarin hukunta wadanda suka aikata laifin, tare da taimakawa wajen samar da kayayyakin agaji ga mutanen da aka kona gidajensu.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro Mike Ejiofor ya ce tilas ne gwamnati ta sauya salon tsarinta domin samun sakamako mai kyau.