Hadakar Rundunar Jami'an tsaro ta Sojoji, 'Yan Sanda da kuma DSS, ta samu nasarar hallaka 'yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane sha biyu (12), a wasu kauyuka da suke Karamar Hukumar Alkaleri, a Jihar Bauchi, arewa maso gabashin Najeriya.
Daga mutanen da aka hallakan, akwai shugaban masu garkuwa da mutane maisuna Madaki Mansur.
Biyo bayan zafafa hare hare ne da wasu 'yan bindiga suka kaddamar a kauyukan da ke Karamar Hukumar ta Alkaleri, cikin satin da ya gabata, hadakar ta kaddamar da yaki da 'yan bindigar a mabuyarsu inda ta yi nasarar hallaka 'yan bindigar da masu satar mutane don karbar kudin fansa, su goma sha biyu a wani matakin tsaro mai taken "Sharar Daji."
A tattaunawa da kakakin Rundunar 'Yan Sanda, Sufurtanda Ahmed Wakil, ta wayar tarho ya yi bayani dangane da nasarar da hadakar Jami’an tsaron ta samu.
Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5