Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Na Ci Gaba Da Bijirewa Dokar Zaman Gida A Kudu Maso Gabashin Najeriya


Jama'a a kudu maso gabashin Najeriya
Jama'a a kudu maso gabashin Najeriya

Jama’a da dama na ci gaba da fita gudanar da harkokinsu a fadin kudu maso gabashin Najeriya duk da cewa wani bangare na kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya tilastawa al’ummar yankin zaman gida na tsawon kwana biyar daga ranar 9 ga wannan watan Disamba.

A wani faifan bidiyon wanda ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta a farkon makon da ya gabata ne kungiyar ta ayyana dokar tare da barazanar hallaka duk wanda ya fito waje daga ranar 9 zuwa ranar 14 ga wata.

Sai dai bayanan da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tattaro na nuni da cewa , daga ranar Jumma’ar da ta wuce, 9 ga wata zuwa yau, mutane da yawa basu janye daga harkokinsu na yau da kullum ba a fadin yankin.

Jama'a a kudu maso gabashin Najeriya
Jama'a a kudu maso gabashin Najeriya

A garin Aba na jihar Abia wani mazauni Malam Idris Bashir ya ce kasuwanci bai tsaya ko na kwana guda ba, yayin da sauran al’umma ke ci gaba da tafiyar da ayyukansu kamar yadda aka saba.

Ya ce, “Anan Aba, gaskiya abin da ya shafi wannan dokar bai ta yi tasiri ba saboda su ‘yan kasuwa sun bijire wa dokar, kuma an ci kasuwa ranar Jumma’a, an ci ranar Asabar, haka kuma ranar Lahadi an yi duk abin da ya kamata a yi.”

Kazalika, ayyukkan yau da kullum basu tsaya ba a jihar Anambra, inji wani mazaunin garin Onitsha Alhaji Yusha’u Imam.

Jama'a a kudu maso gabashin Najeriya
Jama'a a kudu maso gabashin Najeriya

“Tun daga lokacin da aka yi sanarwar zaman gida na kwana biyar a makon da ya wuce, daga ranar Jumma’a zuwa yanzu kowa na ci gaba da kasuwancin sa. Maganar zaman gida babu, kuma ba a yi ba. Yau ma Talata an bude kasuwa, kuma kowa na ci gaba da harkokin sa,” inji Alhaji Imam.

Mista Jude Obike a Owerri, babban birnin jihar Imo, ya bayyana cewa harkoki na ci gaba da gudana, koda yake harin da wasu ‘yan bindiga suka kai shelkwatar hukumar zabe da ke birnin a safiyar Litinin ya hana wasu mutane fitowa.

Ya ce, “Mutane sun lallaba sun fito, sai dai harin da aka kai shelkwatar hukumar zabe ya haddasa tsoro da ya sa har wasu suka noke a gida.”

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG