Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Limamin Juma’a a Taraba


Taraba State Kidnappers
Taraba State Kidnappers

Yan bindiga sun kashe wani babban limanin masallacin Juma’a na unguwar Yelwa dake garin Jatau a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.

A ci gaba da fuskantar rashin zaman lafiya da yan bindiga ke haifarwa a wasu sassan arewacin Najeriya, ‘yan bindiga yi wa babban limamin Juma’a kisan gilla bayan da suka gayyace shi addu’o’in saukar alkur’ani mai girma.

Mai unguwar Yelwa inda lamarin ya faru Mallam Yakubu Yusuf, ya tabbatarwa da sashen Hausa faruwar tashin hankalin ta wayar talho.

Wadanda ke da masaniya kan lamarin sunce daga cikin wasu ‘yan bindiga ne suka gayyaci babban malamin addu’o’in saukar Alkur’ani mai girma a wani kauye dake kusa, bayan zuwansa suka kashe shi tare da sace abin hawar sa.

Muhammad Yakubu ya tsallake rijiya da baya, inda ya ce yayin da suke yi wa malamin rakiya babur din su ya sami matsala, suka tsaya gyara shi kuma ya wuce gaba daga nan sai gawar mallam suka gani.

Hakan ya sa mai unguwa Mallam Yakubu, ke hasashen ‘yan bindigar sun yi amfani da damar gayyata don aiwatar da kisan gilla.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta bakin kakakinta SP Usman Abdullah, za ta kaddamar da bincike kan wannan batu.

Saurari cikakken rahotan Lado Salisu Garba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG