WASHINGTON, D. C. - Wani mai daukar hoto na kamfanin AP da ke cikin jirgin ceton ya ce an dauko mutane 10 a cikin kwale-kwale na kamun kifi na cikin gida sannan wasu 59 kuma jirgin na Indonesia ya ceto su.
Maza, mata da kananan yara, raunana da suke ake jike shataf saboda ruwan sama cikin dare, suna ta kuka a lokacin da aka fara aikin ceto, kuma an dauke mutane a cikin wani jirgin ruwan roba zuwa jirgin ruwan ceto.
Ba a dai san adadin 'yan gudun hijirar dake cikin wannan karamin jirgin ruwan ba a lokacin da ya kife a gabar tekun arewacin Indonesia a ranar Laraba, inda mutane shida da aka ceto da farko suka yi kiyasin mutane 60 zuwa 100 ne.
Babu tabbas ko duka sun yi nasarar manne wa jirgin da ya kife cikin dare ko kuma wasu sun nutse.
Tawagar aikin nema da ceto na Indonesiya sun bar birnin Banda Aceh ne kawai da yammacin Laraba, sa'o'i da yawa bayan kifewar jirgin, kuma da farko sun sha wahala wajen gano jirgin a cikin ruwan da ke gabar teku.
A karshe suka gano jirgin da wadanda suka tsira da tsakar ranar Alhamis.
Amiruddin, shugaban masu kamun kifi a gundumar Aceh Barat, ya ce wadanda aka ceto sun nuna cewa kwale-kwalen na tafiya gabas ne a lokacin da ya fara bulbulo da ruwa cikinsa, sannan karfin ta tura shi zuwa yammacin Aceh. Mutanen shida sun ce wasu na ci gaba da kokarin tsira a kan jirgin da ya kife.
Kimanin ‘yan kabilar Rohingya 740,000 ne dai aka musu matsugunai a kasar Bangaladesh domin gujewa mummunan yakin da jami’an tsaro ke yi a kasarsu ta Myanmar.
Dubban mutane ne ke kokarin tserewa cunkoson sansanoni a Bangladesh zuwa kasashe makwabta inda Indonesia ta ga karuwar ‘yan gudun hijira tun a watan Nuwamba wanda ya sa ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka. 'Yan Rohingya da suka isa Aceh na fuskantar wani kiyayya daga wasu 'yan uwa Musulmi.
-AP