WASHINGTON, D.C. - Lamarin ya auku ne yayin da ‘yan gudun hijirar na Rohingya, wadanda Musulmai ne, ke tserewa matsananincin halin da suke ciki a sansanonin ‘yan gudun hijira a Bangaladesh.
Akalla ‘yan kibilar ta Rohingya miliyan daya ne daga kasar Myanmar suke zaune a sansanin ‘yan gudun Hijra a Bangladesh, cikinsu har da wadanda suka tserewa hare-haren da sojojin Myanmar suka kaddamar tun a shekarar 2017.
Adadin ‘yan Rohingyar da ke ficewa daga Bandgladesh a wannan shekara ya ninku har sau biyar daga abin da aka gani a bara, kamar yadda kungoyoyin kare hakkin bil Adama suka sanar.