Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Tallafin Amurka Na Jin Kai Ga 'Yan Rohingya Da Rikici Ya Shafa


'Yan Gudrun hijirar Rohingya
'Yan Gudrun hijirar Rohingya

Amurka za ta samar da karin kusan dala miliyan 155 a sabon tallafin jin kai don biyan bukatun gaggawa na 'yan gudun hijirar Rohingya da al'ummomin da ke karbar bakunci a Bangladesh, da kuma mutanen da tashin hankalin da ke faruwa ya rutsa da su a jihohin Rakhine, Kachin, Shan, da Chin na kasar Burma.

Akwai kusan 'yan gudun hijira 900,000 a Bangladesh wadanda suka tsere daga mummunan tashin hankali a Jihar Rakhine da ke Burma a cikin shekarun da suka gabata.

'Yan Bangladesh 472,000 da ke cikin al'ummomin da abin ya shafa su ma lamarin ya shafa.

Kuma tashin hankali a Burma ya karu tun bayan juyin mulkin soja da ya kifar da zababbiyar gwamnatin dimokradiyya a watan Fabrairu 2021.

Kasar Amurka ce kan gaba wajen bayar da taimakon jin kai sakamakon matsalar. A lokacin da take sanar da karin taimakon, Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken ya fada a cikin wata sanarwa cewa, da wannan sabon kudin, “gaba daya taimakonmu na jin kai ga wadanda rikicin ya shafa a Burma, Bangladesh, da sauran wurare a yankin tun bayan mummunan tashin hankalin da sojojin Burma suka yi a watan Agustan 2017 ya fi dala biliyan 1.3, gami da sama da dala biliyan 1.1 don shirye-shirye daban-daban a cikin Bangladesh. ”

Ya ayyana tare da nuna godiya ga gudummawar da sauran kasashe membobin Majalisar Dinkin Duniya suka bayar ga ayyukan jin kai, ya kuma bukaci sauran kasashen duniya da su kara taimako.

Sakatare Blinken ya lura da irin tsada da nauyin da kasashe, musamman Bangladesh, suka dauka wajen magance halin da ‘yan gudun hijirar Rohingya ke ciki, kuma ya yi alkawarin tallafawa kasashen yankin da suka ba da fifikon wajen kariyar su.

Ya ce, "Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 1 ga watan Fabrairu da kuma mummunan kisan da sojoji suka yi a Burma," in ji shi, "mun ci gaba da rike alkawarin magance rikicin na Rohingya, ganin cewa shugabannin juyin mulkin da yawa daga cikin mutane ne da ke da alhakin cin zarafin bil Adama a baya, ciki har da ta'asar da aka yiwa Rohingya. Muna ci gaba da aiki tare da kawayen kasa da kasa don tallafawa adalci da bin diddigin duk wadanda ke da alhakin juyin mulkin da kuma take hakkin bil adama. ”

A cewarsa, Amurka, na ci gaba da neman hakkokin 'yan Rohingya tare da yin kira da a sanya su a tattauna game da makomarsu. Sakatare Blinken ya kuma yi kira ga Bangaladash da ta dauki matakan kare 'yan gudun hijirar kuma kada ta bari yanayi ya cigaba "wanda zai tilasta musu komawa kasar da za su iya fuskantar zalunci da tashin hankali."

Sakataren Blinken ya ce "Amurka, ta himmatu wajen inganta zaman lafiya, tsaro da mutunta hakkin bil adama da mutuncin mutane na Burma, ciki har da na yan Rohingya."

XS
SM
MD
LG