Wani mai bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewar, shekaru biyu bayan mummunan korar 'yan gudun hijirar Rohingya sama da dubu 700,000 daga Myanmar, har yanzu babu yanayi mai kyau da zai tabbatar da tsaronsu, saboda kasar na ci gaba da zama mai cike da hatsari a gare su.
Hakan ya sa ake ganin bai kamata su bar matsuguninsu na Cox Bazar da ke Bangladesh ba.
Mai hada rahoto na musamman na Majalisar Dinkin Duniyar, Yanghee Lee, ta ce Myanmar ta ci gaba da keta sabawa dokokin kasa da kasa tana kuma amfani da tsauraran matakai don tursasawa tsirarun kabilu a jihohin Rakhine da kudancin Chin.
Ta ce, an kashe fararen hula da dama kuma dubun dubatar mutane sun tsere sakamakon amfani da manyan bindigogi da sauran hanyoyin muzgunawa ‘yan kungiyar Tatmadaw da sojojin Myanmar da na Arakan su ke amfani da su.
Sai dai wakilin Myanmar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya musanta duk wadannan zarge zarge.
Facebook Forum