Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira da a kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin sojojin kasar Myanmar da na Arakan da ke faruwa a jihohin Rhakine da Chin.
Kiran na zuwa ne yayin da adadin fararen hular da suka mutu sanadiyyar rikicin yake karuwa.
A cewar hukumar, ana samun ‘yan gudun hijirar Rohingya da suka mutu saboda rikice-rikicen, sannan wasu daruruwa sun tsere daga muhallansu inda suka makale a bakin teku na tsawon watanni.
Kakakin hukumar kare hakkin bil adaman Rupert Colville, ya ce karuwar tashe-tashen hankulan da ake gani tsakanin sojojin da ‘yan tawayen na shafar fararen hular kabilu da dama, wadanda ke zaune a Rhakine da Chi, wadanda suka hada da, Chin, Mro, Daignet, Rohingya da dai sauransu.
Facebook Forum