Kusan makonni biyu ke nan da jami'an tsaron Najeriya suka kame wasu 'yan arewa su 486 a kan hanyarsu ta zuwa Fatakwal yin kwadago da neman abun da zasu taimakawa rayuwarsu. An kamasu ne da zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suna shirin kai kari a kudancin kasar.
Matasan sun fito ne daga jihohin Kano, Kaduna, Jigawa da Bauchi amma aka kamasu a garin Aba cikin jihar Abia. A jihar Rivers ne galibinsu ke gudanar da kananan kasuwanci da aikin noma. To saidai shekaranjiya aka saki 144 wadanda aka kammala bincike akansu. Cikin wadannan da aka sake akwai 'yan jihar Jigawa.
Alhaji Aminu Ibrahim Ringim shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar ta Jigawa yayi magana dangane da batun. Yace komenene ake ciki an kamasu amma kuma an sako mafi yawa yanzu kuma suna kan hanyarsu ta komowa gida. Yace maganar ta shafi tsaro ba maganar siyasa ba ce kuma bai kamata a kawo siyasa ciki ba.
Dangane da cewa gwamnatin jihar Jigawa tayi gum da baki akan matsalar 'ya'yanta sai Alhaji Ringim yace duk inda aka ce 'yan Jifawa sun shiga wata matsala gwamnatin jihar ke zuwa ta daidaita ta kwato mutanenta. Haka ma wannan yake. Gwamnatin jihar tayi abun da yakamata tayi domin kwato 'ya'yanta.
Alhaji Ringim yayi harsashen abun da yasa irin wannan lamarin na faruwa da 'yan asalin arewa a kudancin kasar. Yace tabarbarewar tsaro a arewa ta jawo hakan. Da can ba haka abun yake ba. Al'ummar Igbo da Yoruba suna zuwa Jigawa amma babu wanda ya tsaresu domin babu tashin hankali a wurarensu kamar a nan arewa. Yanzu duk inda 'yan arewa suka je mutane na tsoro domin basu san wanene dan ta'ada ba wanene ba dan ta'ada ba.
Yace gwamnatin jihar na duk iyakacin kokarinta domin hana 'yan jihar zuwa cirani a kudancin kasar ko wani wuri ma. Gwamnati na kokarin kirkiro sana'ar da zata sa matasa su kasance cikin jihar. Yanzu suna koyawa matasa sana'o'i. Kawo yanzu sun koyawa matasa fiye da miliyan daya sana'o'i iri iri.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5