Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Mutane 144 Cikin 486 Da Ake Zargin 'Yan Boko Haram Ne


Jami'an Tsaro.
Jami'an Tsaro.

Makon da ya wuce ne jami'an tsaro suka kama wasu 'yan arewa 486 akan hanyarsu ta zuwa Fatakwal da zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne. Lamarin ya jawo cecekuce musamman daga arewa inda ake ganin kamun nada nasaba da kabilanci da addini

A firar da yayi da wakiliyar Muryar Amurka Mike Omeri ya bayyana dalilan da suka sa mahukunta suka tsare mutanen 486 da abubuwan da kuma suke yi da mutanen da yanzu suna tsare a wani sansanin soji.

Yace a cikin binciken da ake yi akan mutanen har an kawo wasu su bada shaida akan wadanda suka sani cikinsu. Ta irin bayanan da suka bayar aka kaiga sakin mutane 144 daga cikinsu.

A cikin binciken mutanen da aka tsare sun ce wani ne ya shirya tafiyar wanda yace zai basu aiki amma su yi gaba zai samesu daga baya. Omeri yace har yanzu jami'an tsaro suna neman mutumin. Da wakiliyar Muryar Amurka ta tambayi Omeri sunan mutumin sai ya ki fada. Yace tunda ana nemansa ba zai fada ba. Amma idan lokacin fadan yayi 'yan jarida zasu ji.

Duk mutanen sun taso ne daga jihar Jigawa kodayake 'yan asalin jihohi daban daban ne a arewa. Akan cewa babu wanda ya taba sa ido akan 'yan kudanci dake tafiya zuwa arewacin kasar sai Omeri yace mutum ya ga motoci 35 iri guda dauke da mutane ko mutum ba dan sanda ba ne zai yi tambaya musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki yanzu.

Ga rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG