Yayin da yake rantsar da kwamishanoni shida gwamnan jihar Gombe Hassan Ibrahim Dankwambo ya bukaci jama'a da su dukufa da yin addu'a domin yanayin da kasar ke ciki.
A lokacin da Musulmai ke shirin fara azumin wannan shekarar gwamnatoci da shugabannin al'umma na cigaba da jawo hankulan mutane dangane da mahimmancin kara dukufa da yin addu'a domin zaman lafiyar kasar.
Gwamnan Jihar Gombe Hassan Ibrahim Dankwambo ya kira al'umma da su dukufa da yin addu'a yayin da yake rantsar da kwamishanoni shida. Yace akwai bukatar kara addu'o'i saboda matsalolin da kasar ta fada ciki. Aikin ibada musamman azumi zai yi wuya idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Shi ma Mr. Mike Omeri shugaban hukumar wayar da kawunan al'umma yace gwamnatin tarayya zata yi duk abun da yakamata ta tabbatar cewa al'ummomi a arewa maso gabas sun gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali da lumana. Yace dokar ta bacin da aka kakaba masu an yi ne domin kare rayukansu da dukiyoyinsu. Ya kira jama'a da su yi hakuri da gwamnati. Yace ba nufin gwamnati ba ne ta kutunta masu. Ya kira mutane da su sa matsalolin kasar cikin addu'arsu domin Allaha Ya kawo saukin lamarin da bada zaman lafiya.
Daga fadar Sarkin Musulmi a can Sokoto an umurci al'ummar Musulmi da su fara duba tsayawar watan azumi daga yau Juma'a.
Ga karin bayani.