Gwamnan jihar Abia ya bada dama a je inda ake tsare da mutanen. Sun je garin sun kuma gana da jami'an tsaro. Yace sabili da shigar gwamnatin tarayya cikin lamarin da dokar da ta shafi irin lamarin ba'a bari sun ga mutanen ba.
Sun gana da jami'an tsaro wadanda suka yi masu bayani cewa saboda doka ba zasu iya ganinsu ba.
To saidai lamarin yana kawo cecekuce ga al'umomin kasar ta Najeriya. Malam Idris Bashir babban limamin Masallacin garin Abia ya bayyana irin bayanin da suke samu akan mutanen. Sun samu bayanin cewa jami'an tsaro na cigaba da bincike.
Dr. Aminu Maude na jam'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto yayi fashin baki dangane da dambarwar. Yace kodayake ana cikin mulkin dimokradiya amma sojoji suna kwace harkokin mulki. An kama 'yan Najeriya kusan dari biyar an ki kaisu kotu an kuma ki sakinsu.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.