Wata cibiyar Kirista wadda Bishop Charles Yohana ke yiwa shugabanci ta shirya taron neman zaman lafiya. Bishop Yahana yace abun takaici ne wasu su bari ana anfani da su wajen kaiwa juna hari lamarin da yanzu ya mayarda yankin kufai.
Bishop Charles Yohana yace sun samu damuwa a cikin Wukari amma Hassan da Husseini ne suka samu damuwa. Yace sun shiga tsakaninsu kuma suna kan sulhuntawa domin a zauna lafiya. Da addu'o'i da hadin kai za'a cimma nasara. Yace damuwar Taraba siyasa ce.
Ita ma kungiyar Miyetti Allah ta tura jakadanta zuwa taron. Husseini Yusuf Boso mataimakin kungiyar na daya yace kungiyar ta turoshi ne ya wakilceta a bangaren shiga tsakani. Yace ya samu kwamitin zaman lafiya karkashin shugabancin Bishop Yohana.
Yusuf Boso yace su Fulani a tarihi basu da fada da Jukun. Ko tsakanin Tiv da Fulani a tarihi basu da fada. Amma abun mamaki wasu marasa gaskiya cikin Tiv da Fulani suka haddasa fada tsakanin kabilun. Manomi da makiyayi duk a daji suke. Sana'arsu iri daya ce da ma'aikata daya. Idan ba zaman lafiya ba za'a yi noma ko kiwo ba. Yace tunda mukaddashin gwamna yana son a zauna lafiya yasa suka zo su ga lallai an taimaka da yin magana da mutanensu. Sun yi kira garesu su rungumi zaman lafiya su kuma daina daukan matakan ramuwa.
Su ma jam'iyyun adawa a jihar sun nuna bacin ransu sabili da rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka. Shugaban APC na jihar yace dole ne al'ummar jihar su rungumi juna. Su hakura su zauna tare . Su fahimtar da juna. Duk wanda yayi laifi a fada mashi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.