Mutanen sun fito ne daga jihohin arewacin Najeriya, wato jihohin Jigawa da Bauchi Mutanen sun ce zasu cirani ne a jihar Rivers.
Sojoji dake da shinge akan hanya ne suka tsaresu kuma suna tuhumarsu da cewa mutanen 'yan Boko Haram ne. Sojojin sun ce sun kame mutanen ne a cikin jerin gwanon motoci da dama lamarin da mutanen suka musanta.
Daya daga cikin direbobin da suka tuko mutanen yace babu kanshin gaskiya cikin abun da sojojin suka fada domin a lokaci daban daban suka taso. Wani Abdullahi Mu'azu mai shiryawa motocin su taso daga Jigawa yace lokuta daban daban motocin ke tashi. Mutanen karkara motocin ke dauka masu zuwa yin aiki ko na noma, dako, gyaran farce, gyaran takalmi, sayar da ruwa da dai makamantansu.
Ikirarin da rundunar sojojin tayi cewa ta samu nasarar kame wani dan Boko Haram da suke nema ruwa a jallo, Bala Mato shugaban kungiyar motoci ya kalubali sojojin. Yace su fito da sunan mutumin da labar motar da yake ciki da dai sauransu.
Ga cikakken rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.