Tsohon shugaban Najeriya Janaral Yakubu Gowon a jawabin da yayi a cibiyar hada magunguna dake Legas yace duk lokacin da ya yi la'akari da abubuwan dake faruwa a kasar sai ransa ya baci ganin yadda alamura suka sukurkuce. Yace Najeriya kasa ce da suka yi gwagwarmaya domin su tabbatar cewa ta zama kasa daya, wato tsintsiya madaurinki daya.
Janaral Gowon yace komi na kasar ya sukurkuce daga koina aka dubeshi. Sabili da haka yace suma masu hada magunguna nada rawar da zasu taka wajen taimakawa al'umma ta cigaba musamman a fannin aikinsu na hada magunguna. Yace wata hanya daya da masu hada magunguna zasu taimaki kasar itace tsaftace magunguna ta yadda za'a fitar da jabun magunguna a kuma hanasu shiga kasar.
Abu daya dake kalubale ga su masu hada magunguna shi ne hada kai da hukumar yaki da miyagun kwayoyi da abinci na kasa inda marigayiya Farfasa Dora Akunyili ta taka rawar gani.
Shi mai aikin magani Ibrahim Ahmed Yakasai daya daga cikin wadanda aka karrama a matsayin fitattun masana hada magunguna na kasa yace da matsalar jabun magani har ta sa kasashe kamar su Ghana da Saliyau da ma wasu sun daina sayen magani a Najeriya. Amma yanzu lamarin ya ragu har ma kasashen sun dawo sayen magunguna a Najeriya.
Shugaban cibiyar Olumide Akintayo akan rawar da cibiyar zata taka domin ta tsaftace miyagun magunguna da miyagun kwayoyi yace zasu yi aiki da kwararrun malamai kuma zasu kai wa duk kamfanoni magungunan da suke bukata su tabbatar babu jabu. Wanda kuma yaki yayi aiki dasu sun san abun da zasu yi.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.