Jirgin saman yayi hatsari ne a tashar jiragen sama ta Unity Oilfield da safiyar yau Laraba yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Juba, babban birnin kasar, kamar yadda ministan yada labaran kasar Gatwech Bipal ya bayyana.

Sudan ta Kudu
Bipal yace fasinjojin jirgin ma’aikatan kamfanin hakar man hadaka na gpoc daya kunshi kamfanin man fetur na kasar China da takwaransa na “Nile Petroleum Corporation” mallakin Sudan ta Kudu.
Ya kara da cewar wadanda suka mutu a hatsarin sun hada da ‘yan China 2 da wani dan Indiya guda.
Bipal bai yi karin haske akan abinda ya sabbaba hatsarin ba.

Sudan ta Kudu
Tunda fari kafafen yada labarai sun bayyana adadin wadanda suka mutu a hatsarin da mutum 18 saidai Bipal ya shaidawa Reuters cewar 2 daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya sun mutu daga bisani. Mutum guda ya rayu.
-Reuters