Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Jirgin Sama Ya Kashe Mutane 61 A Brazil


Plane crash in Barcelos
Plane crash in Barcelos

Sakataren tsaron jama'a na Sao Paulo, Guilherme Derrite, ya tabbatar da cewa babu wanda ya tsira daga cikin mutanen da ke cikin jirgin, da suka kumshi fasinjoji 57 da ma'aikatan jirgin hudu.

Wani jirgin sama dauke da mutane 61 ya yi hatsari a wata unguwar gidajen jama’a da yammacin ranar Juma'a, a birnin Vinhedo da ke kudancin jihar Sao Paulo ta kasar Brazil.

Sakataren tsaron jama'a na Sao Paulo, Guilherme Derrite, ya tabbatar da cewa babu wanda ya tsira daga cikin mutanen da ke cikin jirgin, da suka kumshi fasinjoji 57 da ma'aikatan jirgin hudu. To sai dai shaidun gani da ido sun ce babu wani mutum da ya ji rauni a kasa.

Brazil Plane Crash
Brazil Plane Crash

Kawo yanzu dai ba'a bayyana musabbabin hatsarin jirgin ba. Rundunar ‘yan sandan kasar ta Brazil ta fara gudanar da bincike.

Shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva, ya katse wani taron da yake halarta domin sanar da hadarin.

Kamfanin jiragen sama na VOEPASS ya ce jirginsa, samfurin ATR mai inji 2, ya nufi filin jirgin saman kasa-da-kasa na Sao Paulo, bayan ya bar Cascavel ta jihar Parana ta kasar Brazil.

Bayanan hukumar rajistar jiragen sama ta Brazil sun nuna cewa an kera jirgin na VOEPASS ne a shekara ta 2010, kuma kamfanin jirgin ya saye shi ne a shekarar 2022.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG