Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutum 100 Sun Mutu A Hatsarin Jirgi A Koriya ta Kudu


Ragowar jirgin kamfanin Jeju da ya yi hatsari
Ragowar jirgin kamfanin Jeju da ya yi hatsari

Akalla mutum 177 — mata 84, maza 82, da wasu 11 da ba a iya tantance jinsinsu nan take ba — suka mutu a hatsarin, a cewar hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu.

Wani jirgin saman fasinja ya kama da wuta a ranar Lahadi bayan ya zame daga hanya a filin jirgin saman Koriya ta Kudu kuma ya bugi katanga ta kankare lokacin da birkin gaban taya jirgin ya kasa fitowa.

Mafi yawan mutane 181 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu a cikin daya daga cikin munanan hadarurran jiragen sama na kasar.

Jirgin fasinja na Jeju Air ya yi hatsari yayin da yake sauka a garin Muan, kimanin kilomita 290 kudu da birnin Seoul. Ma'aikatar sufuri ta ce jirgin ya kasance Boeing 737-800 mai shekara 15 da ke dawowa daga Bangkok, kuma hatsarin ya faru da misalin karfe 9:03 na safe.

Akalla mutum 177 — mata 84, maza 82, da wasu 11 da ba a iya tantance jinsinsu nan take ba — suka mutu a wutar, a cewar hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu.

Ma'aikatan gaggawa sun ceto mutane biyu, dukkansu ma'aikatan jirgin. Ma’aikatan kiwon lafiya sun ce suna cikin hayyacinsu kuma ba sa cikin hadarin rasa rayukansu.

Mutane biyu sun bace har bayan awanni tara da faruwar lamarin.

Fasinjojin galibi 'yan kasar Koriya ta Kudu ne, tare da 'yan kasar Thailand guda biyu.

Hukumar kashe gobara ta tura motoci masu kashe gobara 32 da jiragen sama masu shawagi domin dakile wutar.

Kimanin ma’aikatan kashe gobara 1,570, ‘yan sanda, sojoji, da sauran jami’ai sun kasance a wurin, a cewar hukumar kashe gobara da ma’aikatar sufuri.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG