Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iran Ya Rasu A Hatsarin Jirgin Sama


Shugaban Iran, Marigayi Ebrahim Raisi
Shugaban Iran, Marigayi Ebrahim Raisi

Gidan talbijin na State TV bai fadi abin da ya haddasa hatsarin ba wanda ya auku a gabashin lardin Azerbaijin.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen kasar da wasu mutane sun rasu bayan da jirgin da suke ciki mai saukar ungulu ya yi hatsari.

An gano gawarwakinsu ne bayan da aka kwashe sa’o’i ana nemansu a wani yanki mai tsaunuka da hazo ya lullube.

Gidan talbijin na State TV bai fadi abin da ya haddasa hatsarin ba wanda ya auku a gabashin lardin Azerbaijin.

Raisi na tare ne da ministan harkokin wajen Hossein Amirabdollahian, gwamnan Iran na gabashin Lardin Azarbaijin da wasu jami’ai da masu tsaron lafiyarsu, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar na IRNA.

Hukumomin Turkiyya sun saki wani hoton bidiyo wanda ya nuna kamar wuta na ci da ake fargabar tarkacen jirgin ne.

Da masu kai dauki suka isa wajen tarkacen jirgin an tarar babu alamar wani da ke da rai.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG