Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Kudu Ta Kaddamar Da Binciken Lafiyar Jiragen Samanta Bayan Mummunan Hatsarin Da Ya Kashe Mutane 179


Jirgin saman Jeju Air Boeing 737-800 da ya kama da wuta bayan ya bugi wani bango a tashar jirgin saman Muan International Airport a South Jeolla Province, Dec. 29, 2024.
Jirgin saman Jeju Air Boeing 737-800 da ya kama da wuta bayan ya bugi wani bango a tashar jirgin saman Muan International Airport a South Jeolla Province, Dec. 29, 2024.

A yau Litinin Shugaban Koriya ta Kudu na riko, Choi Sang-Mok ya bada umarnin gaggauta duba lafiyar ilahirin ayyukan jiragen saman kasar a dai-dai lokacin da masu bincike ke aikin tantance mutanen da hatsarin jirgin sama mafi muni a kasar ya rutsa dasu, dama abinda ya sabbaba shi

Ilahirin fasinjoji 175 da 4 daga cikin ma’aikatan jirgin saman Jeju Air sun hallaka sa’ilin da jirgin ya rikito a tashar jiragen saman kasa da kasa ta Muan, inda ya kama da wuta bayan da ya afkawa wata katanga.

An yi nasarar kubutar da ma’aikatan jirgin 2 da ran su.

Jirgin Korea ta Kudu da yi hatsari a tashar jirgin saman Muan
Jirgin Korea ta Kudu da yi hatsari a tashar jirgin saman Muan

Abin da zamu fi baiwa fifiko a halin yanzu shine tantance bayanan mutanen da hatsarin ya rutsa dasu, da tallafawa iyalansu da kuma baiwa mutane 2 da suka kubuta kulawar data dace, kamar yadda Choi ya shaidawa wani taro akan tunkarar bala’o’i a birnin Seoul.

“Tun kafin a fitar da sakamakon karshe, mun bukaci jami’ai su gudanar da binciken dalilin afkuwar hatsarin a bayyane tare da gaggauta sanarda iyalan da suka rasa wani nasu,” a cewarsa.

“da zarar an kammala binciken afkuwar hatsarin, an bukaci ma’aikatar sufuri ta gudanar da binciken gaggawa akan lafiyar ilahirin tsarin sufurin jiragen saman kasar domin kaucewar afkuwar hatsarin jirgin sama anan gaba,” a cewar Choi.

A matsayin matakin farko, ma’aikatar sufuri ta sanarda shirinta na gudanar da binciken musamman akan dukkanin jiragen sama 101 samfurin Boeing 737-800 da kamfanin jiragen saman Koriya ta Kudu ke aiki dasu tun daga yau Litinin, inda zasu maida hankali akan tarihin gyare-gyaren da aka gudanar akan muhimman bangarori.

Jirgin saman Jeju mai lamba 7c2216, dake dawowa daga Bangkok, babban birnin kasar Thailand, na kokarin sauka ne a filin saukar jiragen saman dake kudancin kasar a jiya Lahadi sa’ilin da hatsarin ya afku.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG