Rahotanni daga Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wani jirgin saman sojin kasar mai saukar ungulu ya yi hatsari da safiyar Litinin.
Hatsarin ya faru ne a kusa da kauyen Tiami da ke karamar hukumar Igabi da ke jihar.
Babu asarar rai a cewar rahotannin da kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa matukin jirgin ya yi nasarar ficewa ba tare da wani mummunan rauni ba.
Jaridar Daily Trust a hirar da ta yi da wani mazaunin yankin ta ce jirgin ya fadi ne da misalin karfe biyar na safiyar Litinin bayan da ya fuskanci matsala.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin sojin saman kasar ba su ce uffan ba kan wannan hatsari.
Amma bayanai sun ce tuni jami’an tsaro sun killace yankin da jirgin ya fadi don gudanar da bincike.
Yankin kauyen na Tiami da jirgin ya fadi ba shi da tazara mai nisa daga hedkwatar horar da matuka jirgin saman sojin Najeriya da ke yankin Mando a karamar hukumar ta Igabi.
Hatsarin jirgin sama mafi muni da ya shafi sojin Najeriya da ya auku a baya-bayan nan shi ne wanda ya halaka mutum 11 ciki har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Ibrahim Attahiru a watan Mayun 2021.
Dandalin Mu Tattauna