Tagwayen Bamabamai Sun Tashi a Wani Masallaci dake Maiduguri Jihar Borno

Wasu da suka samu rauni a harin bamabamai a Maiduguri

Cikin daren jiya wasu tagwayen bamabamai suka tashi a wani masallaci dake anuguwar Malai a Maidugurin jihar Borno.

Anguwar Malai tana dap da shiga birnin Maiduguri ne nan bamabaman suka tashi suka kuma yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu.

Tashin bamabaman ya zo ne bayan kwana biyu da aka samu tashin wasu bamabaman a anguwar Sajeri da suka hallaka rayukan mutane hudu da kuma raunata guda goma sha uku.

Cikin 'yan kwanakin nan al'ummar birnin Maiduguri na cigaba da fuskantar matsalar hare-haren bamabamai sanadiya kutsawa cikin jama'a da 'yan kunar bakin wake ke yi.

Amma bam din da ya tashi a anguwar Malai ana kyautata zaton an boyeshi ne kana aka tada shi a daidai lokacin da ake sallar magaruba.

Wani ganao ya shaidawa Muryar Amurka cewa wadanda suka mutu zasu kai kamar mutane goma banda wadanda suka ji rauni. Bam na farko da ya tashi ya sa masallacin ya rushe kan mutane. Ana kokarin taimaka masu kuma sai na biyun ya tashi.

Da alamu 'yan Boko Haram suna sake kama suna shiga jama'a suna aikata ta'adanci. Ko a Gwozah shekaranjiya wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun shiga garin sun yiwa wasu mutane tara yankan rago.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tagwayen Bamabamai Sun Tashi a Wani Masallaci dake Maiduguri Jihar Borno - 3' 10"