Irin wannan tashin boma boman dai kan tashine a masallatai ko gurin kasuwanci ko kuma wajen hada hadar jama’a, wanda akasari akan zargi kananan mata ne da kaiwa don kashe kansu dama sauran mutanen dake a guraren. Wadanda ke da sauran kwana kuma su kan fada mawuyacin hali, sakamakon irin munanan raunukan da jama’a ke samu.
Sai dai duk da tashe tashen boma boman babu wata kungiya da ta fito don daukar irin wadannan hare haren. Sai dai a baya kungiyar Boko Haram kan dauki nauyin irin wadannan tashin boma bomai, da kanyi sanadiyyar mutane masu dinbin yawa. Bayan hawa kan kujerar mulki shugaba Buhari ya umarci rudonin sojan Najeriya da su kawo karshen wannan ta’addancin da ya addabi mutanen dake shiyar Arewa maso Gabas din Najeriya.
Ganin yadda har yanzu akan sami tashin boma bomai a nan da can, hakan yasa wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya nemi jin ta bakin jama’a kan yadda suka ganin wannan al’amari, kuma rundunar sojan Najeriya na samun nasara kan wannan yaki da suke gudanar wa a halin yanzu.
Mutane dayawa na ganin ana samun ci gaba ga wannan yaki da ake, harma suna gani gwamnati da rundunar sojojin Najeriya na aikin da ya kamata.
Saurari cikakken rahotan.