Kare jini, biri jinni da dakarun Najeriya keyi da ‘yan ta’adda a tarihi, wanda ya kaiga nasarar dawo da zaman lafiya a Saliyo, da Liberiya, da Sudan harma da Tallafi ga Mali, ya zama mai daure kai, inda tamkar dakatar da zubar da jinin ya gagari jami’ai a Najeriya.
Kungiyar rajin ‘yancin bil adama ta Amnesty International ta fitar da wasu hotunan bidiyo dake nuna Sojoji suna yanka fararen hula, wadanda aka zarga a cewar na Najeriya ne. Ta bakin kakakinta, Major Chris Olukolade, rundunar sojan Najeriya taki amincewa da wadannan hotunan bidiyo.
“Koma dai yaya, gaskiyar zata bayyana, amma sam babu sakacin aikin dakarunmu a akasin,” fassarar kalaman Olukolade wanda yayi da turanci.
Mr. Kolade ya kara da cewa ‘yan ta’adda na aiki da hanyar kunar bakin wake wajen cimma burinsu, amma haka ba zai firgita jami’ai su daina aikinsu ba.
Da alamu ko an samu salama, illar wadannan rigingimu zasu cigaba da yin fatalwa na tsawon zamani.
Your browser doesn’t support HTML5