Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dimbin Mutane a Wasu Kauyuka 3 Daf da Chibok


'Yan boko haram ake zargi da kai hare-haren.
'Yan boko haram ake zargi da kai hare-haren.

Maharan da ake jin cewa 'yan Boko Haram sun kai farmaki kan Majami'u da wasu kauyuka a kusa da Chibok.

Wadansu maharan da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe dimbin mutane a ranar Lahadi cikin wani harin da suka kai kan kauyuka uku, da kuma wani harin da suka kai kan masu ibada a wata Majami'ar da ke kimanin tazarar kilomita biyar da garin Chibok inda 'yan kungiyar suka sace 'yan mata dalibai fiye da dari biyu.

Bello Habeeb Galadanchi ya tuntubi wakilin Sashen Hausa a Borno, Haruna Dauda Biu wanda yayi karin bayani kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

A wani hari na daban kuma da yammacin Jumma'a 'yan ta'addan sun halaka sojoji bakwai a kauyen Goniri, a jahar Yobe a cewar wata majiyar jami'an tsaro da wani shaida.

Maharan sun kai farmakin na ranar Lahadin ne a kusan lokaci guda kan kauyukan uku da ke karamar hukumar Chibok a jahar Borno.

Wani shaida da ya tsira daga harin da suka kai kauyen Kautikiri, Samuel Chibok, ya ce mahara maza kimanin su ishirin ne a cikin wata mota a kori kura samfurin Toyoya, sauran kuma akan babura suka shiga garin, suka yi ruwan harsashai kan mutanen da ke cikin wata Majami'a su na ibada.

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG