Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Janar na Sojan Amurka


Afganistan
Afganistan

Wani mutumi sanye da kayan sojan Afghanistan ya bude yau talata ya kashe wani janar na sojan Amurka.

Wani mutumi sanye da kayan sojan Afghanistan ya bude yau talata ya kashe wani janar na sojan Amurka, ya raunata wasu sojojin na Amurka da na kasashen waje da dama, a wani lamarin da ake baynnawa a zaman harin cikin gida na baya bayan nan daga sojojin Afghanistan.

Sakataren yada labarai na ma'auikatar tsaron Amurka, Rear Admiral John Kirby, ya fadawa 'yan jarida a Washington cewa an kashe wani janar na sojan Amurka, amma bai bayyana sunansa ba.

Wannan sojan Amurka mai mukamin Manjo-Janar, wanda shi ne soja mafi girman mukami na Amurka da aka taba kashewa a Afghanistan, an ce an harbe shi kusa da kusa sosai a lokacin da ya kai ziyara zuwa Jami'ar Tsaron Kasa ta Marshall Fahim a Kabul.

Wadanda suka ji raunin sun hada da wasu sojojin kasashen waje dake Afghanistan, cikinsu har da wani Birgediya-Janar dan kasar Jamus.

Ma'aikatar tsaron Afghanistan ta ce an kashe wannann maharin da ta bayyana a zaman dan ta'adda sanye da rigar sojan Afghanistan.

Shugaba Hamid Karzai yayi Allah wadarai da wannan harbin, ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan dukkan wadanda abin ya shafa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG