Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mata ta Fasa Bam a Gidan Mai a Kano


'Yansanda a wurin da Bam ya fashe.
'Yansanda a wurin da Bam ya fashe.

Tuni dai jami’an ‘yansanda da sojoji suka yi ma wurin kawanya tare da kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Wata mata mai matsakaicin shekaru ce ta je gidan man da bam like a jikinta kuma ta tinkari bangaren da mutane suka yi jerin Gwano domin sayen kalanzir. Nan take dai bam din ya tashi da it, ya kuma hallaka mutam biyar tare da jikkata wasu da yawa.

Tuni dai jami’an ‘yansanda da sojoji suka yi ma wurin kawanya tare da kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke tsakiyar birnin Kano.

Sai dai kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya bai ce uffan ba dangane da al’amarin. Yace ba a bashi izinin Magana da ‘yan jarida ba tukunna.

Harin na hotoro shine na 3 a Kano tun daga kamala salar idi jiya zuwa yau. Wani Bam ya fashe a dab da gidan Murtala kuma ya raunata ‘yansanda guda 4 kana daga bisani, wani sabo ya sake fashewa a zungere road da ke ‘yankin kasuwar sabon gari wanda yayi sanidiyar mutuwar mutane 5, mutane 8 kuma suka jikkata.

Kwamishinan kiwon lafiya Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya umurci jami’an kiwon lafiya da su kula sosai da wadanda suka ji jiki a asibitocin gwamnati

Yanzu haka dai manyan ‘yan kasuwa da sauran ‘yan arewacin Najeriya sun fara kokawa dangane da rikon sakainar kashin da suka ce hukumomi na yi ma sha’anin tsaro a lardin na Arewa.

Dab da kamala wannan ruhoton, sai aka sami labarin fashewar wani bam din a bakin katafaren kanti ShopRite da ke kan titin zuwa gidan zoo. Sai dai har yanzu babu adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata.

Ruhoton wakilin muryar Amurka Mahmood Ibrahim kwari ke nan a kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG