Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Sun Kai Hare-hare Kan Wasu Kauyukan Jihar Adamawa


Wuraren da aka kai hare-hare
Wuraren da aka kai hare-hare

Rahotanni daga jihar Adamawa na nuni da cewa wasu kauyukan kananan hukumomin Gombi da Madagali da Hong sun kwana 'yanbindiga na kai masu hare-hare.

'Yanbindigan sun farma wasu kauyuka a kananan hukumomin inda kawo yanzu ba'a iya tantance asarar rayuka da dukiyoyi da al'ummomin wuraren suka yi ba.

Kauyukan da aka kaiwa hare-hare sun hada da Zha da Muben da Luben duk a karamar hukumar Hong. Kawo yanzu ba'a gano dagacin garin Zha ba Wing Commander Dauda Daniel mai murabus. Wani ganao yace an kashe akalla mutane 28 a wasu wurare biyu.

Kafin wannan harin sai da 'yanbindigan suka kai hari a wasu kauyukan Madagali inda suka yi awon gaba da shanu da abinci. Yayin harin a kauyen Kuda an ce sun kashe mutane shida.

Ana cikin wannan alhini sai kawai kuma ga wata sabuwa inda 'yanbindigan suka yi kukan kura akan yankin Garkida dake cikin karamar hukumar Gombi. Kwana kwanan nan 'yanbidiga suka sace wani Bajamushe a Gombin kuma har yanzu yana hannunsu.

Harin da suka kai cikin dare sun farma sojoji da 'yansanda. Wani mazauna garin ya bada shaidar lamarin da ya faru. Akwai sassan sojoji tsakanin Borno da Adamawa. Da 'yanbindigan suka isa yankin sai suka fara kai hari akan sojojin. Bayan sun kwashe wajen mintuna talatin suna fafatawa da sojoji sai suka shiga Garkida inda suka fara kai hari a asibitin da sojoji suke.

Hukumomin tsaro sun ce suna iyakacin kokarinsu wajen shawo kan lamarin kamar yadda kakakin 'yansandan jihar Adamawa ya fada. Yace sun tura jami'an tsaro koina kuma yanzu kura ta lafa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG