Sojojin Mulkin Nijar Sun Ba Jakadan Faransa Sa'o'i 48 Ya Fice Daga Kasar

Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Hukumomin Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar a cikin sa'o'i 48 daga ranar Juma’a 25 ga watan Agusta, sai dai ma’aikatar harakokin wajen Faransa a na ta bangare ta yi watsi da matakin.

NIAMEY, NIGER - Rashin amsa gayyatar da Ministan harakokin wajen Nijar ya yi wa jakadan Faransa Sylvain Itte domin ya amsa wasu tambayoyi a jiya Juma’a 25 ga watan Agusta, ya sa ofishin Ministan Gwamnatin rikon kwaya ta kasar ba shi umurnin ficewa daga kasar kafin shudewar wa’adin kwanaki biyu wato sa'o'i 48, kamar yadda ya ke a takardar da aka aika wa ofishin jakadancin Faransa da ke brinin Yamai.

Kungiyar M 62 wacce ta jima ta na fafutuka kan bukatar ganin Nijar ta kwatar wa kanta cikakken ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka ta yaba da wannan mataki a cewar Falmata Taya wacce jigo ce a kungiyar ta M 62.

To sai dai ra’ayoyi sun sha bamban kan wannan batu domin a ra’ayin wani jigo a jam’iyar PNDS, Sahanine Mahamadou an yi kuskure wajen yanke wannan shawara.

A martanin da ta mayar sa’oi kadan bayan bayyanar wannan mataki, Gwamnatin Faransa ta yi watsi da shi saboda dalilai masu nasaba da abin da ta kira rashin hallaccin mahukuntan Nijar na yau.

Saboda haka a yanzu dai babu inda jakadan zai tafi sakamakon rashin aminta da hukumomin mulkin sojan kasar da Faransa ta ce ba su da halacci da rike iko.

Tun a washe garin juyin mulkin 26 ga watan Yuli ne aka shiga takun saka a tsakanin Gwamnatin Faransa da sojojin Majalissar CNSP. Yayin da Faransar ke matsin lamba akan su mai da zababben Shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa, sojojin a na su bangare sun tsinke dukkan wata yarjejeniyar ayyukan soja da ke tsakanin kasashen biyu, sannan sun umarci kasar da ta yi wa Nijar din mulkin mallaka da ta kwashe dakarun da ta girke a kasar da sunan yaki da ta’addanci.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Mulkin Nijar Sun Baiwa Jakadan Faransa Awoyi 48 Ya Fice Daga Kasar.mp3